✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dangote ya tafka asarar Naira biliyan 342 a cikin sa’o’i 24

Hakan dai ya sa ya sauka daga mataki na 106 a duniya zuwa na 114 a jerin attajiran duniya.

Hamshakin attajirin nan na Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya tafka asarar da ta kai Dalar Amurka miliyan 900, kwatankwacin Naira biliyan 342 a cikin sa’o’i 24.

Hakan dai ya biyo bayan asarar da kamfaninsa ya tafka a karshen rufe kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya a ranar Juma’a.

Jerin sunayen attajirai 500 da kafar yada labarai Bloomberg take wallafawa ya nuna cewa kudaden Dangote sun sauka daga Dala biliyan 18 da miliyan 400 zuwa Dala biliyan 17 da miliyan 500.

Dangote ne dai kadai dan Najeriyan da ya shiga jerin hamshakan attajirai 500 na duniya, yayin da har yanzu kuma yake ci gaba da rike kambunsa a matsayin na daya a nahiyar Afirka.

Hakan dai ya sa ya sauka daga mataki na 106 a duniya zuwa na 114 a jerin attajiran duniya.

A ranar 13 ga watan Disambar bara, kudaden Dangote sun karu da Dala biliyan 15.5, inda ya kare shekarar 2020 yana da Dala biliyan 17.8.

Kazalika, attajirin ya sami karuwar Dala miliyan 600 a kwanaki bakwai na farkon 2021, amma ya yi asarar dukkansu a ranar Juma’ar da ta gabata.

“Akasarin tattalin arzikin Dangote ya fito ne daga siminti wanda ya dauki kusan kaso 86 cikin 100. Shine ya mallaki kaso mafi tsoka na kai tsaye na hannun jarin kamfanin, ta hanyar rukunin kamfanoninsa na Dangote,” inji ja Bloomberg.

Daga nan sai kamfanin sarrafa takin zamani wanda yake da karfin sarrafa tan miliyan 2.8 a kowacce shekara.

“Sai dai ba a hada da matatar man fetur dinsa ba ta kusanHakan dai ya sa ya sauka daga mataki na 106 a duniya zuwa na 114 a jerin attajiran duniya. Dala biliyan 12 wacce har yanzu ake aikin gina ta kuma ba ta fara aiki ba a cikin jerin kadarorin da attajirin ya mallaka,” inji jaridar.