Babban attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana goyon baya ga tsohuwar Ministar Kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala a takarar Shugaban Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO).
Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote ya ce babu wanda ya fi cancanta ya shugabanci WTO a cikin ’yan takarar sama da Ngozin.
“A wannan yanayin da ake ciki mai cike kalubale iri-iri, WTO na bukatar mutum mai tarin ilimi da kuma kwarewa ta musamman kamar Misis Ngozi Okonjo Iweala ya jagoranceta domin tabbatar da karfafa cinikayya a duniya.
“Zabarta a mukamin shi ne abin da ya dace a wannan lokacin. Na yi na’am da takararta domin ta jagoranci WTO”, inji Dangote ta shafinsa na Twitter a ranar Talata.
- Yadda ‘yan kasashen waje ke juya farashin fulawa a Najeriya
- Mujallar Charlie Hebdo ta kara yin batanci ga Manzon Allah
- ‘Ya kamata Majalisa ta taka wa Buhari burki kan ciwo bashi’
Ngozi ya yi wa Dangote godiya
A nata bangaren, Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana farin ciki da goyon bayan dan Dangote ya nuna mata, inda ba da jumawa ba bayan ya bayyana goyon bayanta ita ma ta wallaf sakonta na godiya.
“Ina godiya, dan uwana Aliko da wadannan kywawawan kalamai masu ban mamaki. A matsayinka da fitaccen dan kasuwa a duniya da fahimtarka game da WTO, ina matukar godiya game da kwarin gwiwar da kake da shi a kai na”, inji ta.
Yadda ake zaben WTO
Ngozi mai kimanin shekaru 66 na hankokorn darewa kujerar da dan asalin kasar Brazil, Roberto Azevedo ya ke shirin bari.
Duk dai wanda ya samu damar darewa kujerar, akwai jan aiki a gabansa na ganin ya sasanta tsakanin kasashen China da Amurka, ya kawo sauye-sauye a harkokin kasuwancin duniya musamman a lokacin da duniya ke kokarin murmurewa daga masassarar annobar COVID-19.
A al’adance dai WTO ce ke zabar shugabanta ta hanyar tattaunawa yayin da ake kada kuri’a ne kawai idan hakan ta ki samuwa.