✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangin matar da suka ce an cire wa sassan jiki a asibitin Gombe sun lashe amansu

Sun ce sun gamsu ne bayan yin bincike a asibitin

Dangin Halima Ibrahim, marigayiyar nan da aka yi zargin an cire wa al’aura da ido ɗaya a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke Gombe, sun lashe amansu.

A ranar Talatar da ta gabata ce dai wasu ’ya’ya da dangin marigayiyar mai shekara 61 suka yi bore a kofar shiga asibitin, bisa zargin cire sassan jikin marigayiyar.

Amma a ranar Laraba kuma hukumar asibitin tare da dangi da malaman coci da likitan iyalan da kuma shugabancin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) suka bayyana wa manema labarai cewa bayan gudanar da gwaji na kwararru sun gano ba a cire ido ko wani sashin jikin gawar ta su ba kamar yadda wasu ’ya’yanta suke zargi.

Sun bayyana matsayin ne bayan gudanar da gwaji da binciken ƙwaƙwaf kan gawar matar.

Wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayiyar Bilyaminu Dogara Kambel, ya ce gwaje-gwaje da hukumar Asibitin ta gudanar a gabansu ya karyata zargin cewa an cire wa gawar mahaifiyar tasu ido ko al’aurar ta kamar yadda a baya suka yi zargi.

Bilyaminu Dogara, ya kara da cewa a gabansu aka gudanar da duk wani gwaje-gwajen.

Ya ce, “Korafinmu shi ne me ya janyo aka cire fatar saman girar idonta? Me za a yi da shi, shi ne kukanmu,” in ji shi.

Shi ma malamin Cocin da marigayiya Halima take ibada a ciki, Rabaren Agai Arab Audu, ya ce sun gamsu da bayanan asibiti na sakamakon gwajin da ya tabbatar idon marigayiyar yana nan ba a cire ba, fatar saman girar idon ne aka cire.

Shi ma Shugaban CAN na Jihar Gombe, Rabaren Alphonsus Yusuf Shinga, ya ce a lokacin da matasa ke boren a kofar shiga asibitin, jami’an ’yan sanda sun kira shi yaje ya kwantar musu da hankali ya rarrashe su akan kada su dauki doka a hannunsu.

A bangaren hukumar asibitin, Shugaban shi, Farfesa Yusuf Abdallah, wanda mataimakinsa, Farfesa Adamu Danladi Bojude ya wakilta ya bayyana cewa bayan rasuwar marigayiyar ce wasu suka shiga kafar sada zumunta na zamani suka dinga cewa an cire wa gawa ido da al’aura a asibitin wanda kuma ba gaskiya ba ne.

Farfesa Bojude, ya kara da cewa yanzu haka asibitin ya kafa kwamitin da ya kunshi ’yan uwar marigayiyar da likitan su, Ahmadu Dangana da malaman cocinsu su da kuma kungiyar CAN da jami’an tsaro wanda aka gudanar da gwajin a gabansu suka kuma gamsu da cewa ba abin da ya sami sassan jikin marigayiyar.

Daga nan sai ya bukaci al’umma da su rika tantance sahihancin labarin da suka samu musamman a kafafen sada zumunta kafin su yada, sannan su guji daukar doka a hannunsa.