A duk lokacin da aka ambanci sunan ‘Pele’ babu bukatar sharhi kafin a san wanda ake batu saboda shahara da mai sunan ya yi a duniyar kwallon kafa.
Asalin sunansa, shi ne Edson Arantes do Nascimento (Pele) daga kasar Brazil, kuma ya yi shuhura a harkar kwallon kafa wanda har yanzu babu kamar sa a duniya.
- Ku dauki makamai ku kare kanku daga ’yan bindiga – Gwamnan Bauchi
- NAJERIYA A YAU: Yadda Karin Albashi Zai Shafi Rayuwarku
Baya ga ficen da talikin ya yi a duniya, akwai wata alaka tsakaninsa da Najeriya wanda da daman ’yan kasar ba su san da ita ba, duk da cewa tarihin kasar ba zai mance da ita ba.
Ko mai karatu na sane da cewa Pele ya taba ziyartar Najeriya, har ma aka tsagaita wuta a yakin basasar da kasar ta fuskanta tsakanin 1967 da 1970 albarkacin ziyarar tasa?
Gwarzon dan kallon ya ziyarci Najeriya a watan Janairu, 1969 lokacin da ake tsaka da gwabza yakin Biafra inda ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Brazil (Santos) domin buga wasan sada zumunta da takwararta ta Najeriya da ake kira da Green Eagles a wancan lokaci.
Wannan ya yi sanadin da aka ajiye makamai na tsawon sa’o’i 48 don bai wa ’yan kasa damar zuwa kallon wasannin da aka buga a Legas da Benin.
Pele da tawagarsa sun iso Najeriya ne ranar 26 ga Janairu ana tsaka da yakin basasar, inda aka tashi ci 2-2 a wasan da aka buga a Legas, sannan Brazil ta doke Najeriya da ci 2-1 a fafatawar da aka yi a Benin (tsohuwar Jihar Bendel).
Rahotanni sun nuna, kimanin mutum 25,000 ne suka shiga kallon wasan da aka buga a Benin.
Wannan ya yi dalilin da Gwamnan soji na Jihar Bendel a wancan lokaci, Samuel Ogbemudia, ya ba da hutun kwana daya tare da bude gadar da ta hada Benin da yankin Biafra.
Bayan kammala wasannin Pele suka bar kasar, daga nan kuma yakin basasar ya dora daga inda ya tsaya aka ci gaba da fafatawa.
Kazalika, Pele ya sake dawowa Najeriya a ranar 26 ga Afrilu, 1978, tare da kungiyar kwallon kafa ta Brazil wato Fluminese, inda suka buga wasan sada zumunta da Racca Rovers a Filin Wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.
A wannan karon har karrama shi Gwamnan Soji na Jihar Filato na wannan lokaci, Air Commodore Dan Suleiman, ya yi inda ya sanya masa babbar riga da hula Zanna Bukar.
A ranar Alhamis aka ba da sanarwar mutuwar gwarzon lamarin da ya girgiza duniyar kwallon kafa.
An haifi Pele ne a ranar 23 ga Otoba, 1940 inda ya bar duniya yana da shekara 82.
Marigayin ya lashe Kofin Duniya sau uku a halin rayuwarsa.