✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Dan Yahoo’ ya kashe budurwarsa, ya banka wa otel wuta

Dan Yahoo ya banka wa dakin otel wuta bayan ya kashe karuwarsa a a ciki.

Wani wanda ake zargin dan damfara da itanet ne, wato dan Yahooو ya caka wa wata karuwa wuka ya kashe ta a wani otel.

Dan Yahoo din, wanda ya tsere bayan ya yi aika-aikan ya kuma banka wa dakin otel din da suka kama da yarinyar da ya dauka wuta.

Majiyoyi sun ce, “Ba mu san mutumin ba, ba mu san abin da ya faru ba, amma mun tsinci gawar yarinyar.

“Tserewa ya yi bayan abin da ya aikata, saboda haka muna so ’yan sanda su kama shi domin ya fuskanci hukuncin kashe ta da ya yi.”

An gano danyen aikin nasa ne bayan hayaki ya turnike otel din daga dakin da ya kama tare da yarinyar tasa.

Wannan lamari dai ya faru ne a kan titin Nnebisi da ke Asaba, babban birnin Jihar Delta.

Kakakin ’yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ta tabbatar wa wakilinmu da faruwar lamarin, amma ta ce sai daga baya za ta yi karin bayani.

%d bloggers like this: