✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan wasan tsakiyar Chelsea Jorginho ya koma Arsenal

Arsenal ta kammala cinikin dan wasan Italiya da Chelsea Joginho kan fam miliyan 12.

Arsenal ta kammala cinikin dan wasan Italiya da Chelsea Joginho kan fam miliyan 12.

Joginho mai shekaru 31 ya aminta da yarjejeniyar watanni 18, da kuma damar tsawaita zaman nasa daga nan.

An kammala yarjejeniyar ce bayan Jorginho ya tsallake matakin auna koshin lafiyarsa da aka gudanar a safiyar wannan Talatar.

Arsenal mai jan ragama a teburin Firimiyar Ingila a kakar wasannin bana, za ta biya Chelsea farashin fam miliyan 10 kan dan wasan da kuma karin wasu tsarabe-tsarabe na fam miliyan biyu.

Cikin sanarwar bakwana da Chelsea ta fitar, ta bayyana Jorginho a matsayin jagora a ciki da wajen filin tamaula.

Chelsea ta ce ba za a mance da Jorginho ba musamman dangane da irin nutsuwarsa tun bayan zuwansa kungiyar ta Yammacin Landan daga Napoli.

Akwai yiwuwar Jorginho zai haska karon farko yayin da sabuwar kungiyarsa za ta je bakunta Everton a wasan Firimiyar Ingila a ranar Asabar.