Dan takarar Sanata a mazabar Katsina ta Arewa a jam’iyya mai mulki ta APC Ahmad Baba Kaita ya fadi a rumfar zaben Shugaba Muhammadu Buhari’s da ke unguwar Sarkin Yara Ward A, da rumfar zabe ta Kofa Baru (03), da rumfar zabe ta Gidan Niyam duk a karamar hukumar Daura da ke jihar Katsina.
Jam’iyyar Accord Party (AP) ce ta lashe zaben rumfunan.
Jam’in zaben Aliyu Abdullahi ya sanar da sakamakon zaben sanatocin kamar haka: Dan takarar APC Ahmad Baba Kaita ya samu kuri’u 247, dan takarar PDP Mani Nasarawa ya samu kuri’u 2, yayin da dan takarar AP Mohammed Lawal Nalado ya samu 262.
A bangaren sakamakon ‘yan takarar Shugaban kasa, shugaba Buhari ya lashe rumfar zabensa da kuri’u 532 yayin da dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya samu kuri’u 3.