✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar NNPP ya nemi kotu ta hana INEC kammala zaben Doguwa/Tudun Wada

Salisu Yusha'u ya bukaci kotu da dakatar da INECkwana 10 kafin a yi karashen zaben

Dan takarar Jam’iyyar NNPP a zaben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Salisu Yusha’u, ya bukaci kotu da dakatar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) daga gudanar da karashen zaben yadda hukumar ta shirya.

Dan takarar, wanda ke kalubalantar sakamakon zaben da INEC ta sanar da farko ya nemi kotu ta hana hukumar gudanar da karashen zaben ne kwana 10 kafin 15 ga watan Afrilun da muke ciki da hukumar ta sanya domin shi da sauran zabukan da ba su kammalu ba a sassan Najeriya.

A takardar karar da Salisu Yusha’u ya shigar ta hannun lauyansa, Adegboyega Awolomo, ya ce, INEC, “Ba ta da ikon gudanar da karashen zaben alhali ya shigar da karar kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu.”

Idan ba a manta ba, INEC, ta ayyana zaben kujerar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada a Jihar Kano a matsayin wanda bai kammala ba, saboda kuri’un da aka soke a zaben sun haura tazarar da ke tsakanin Salisu Yusha’u da kuma, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Honorabul Alhassan Ado, wanda ya samu kuri’u mafiya rinjaye.

Da farko INEC ta bayyana Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara, amma daga bisani baturen zaben ya janye sanarwar, saboda tazarar da Doguwa ya ba wa Yusha’u ya bai kai yawan kuri’un da aka soke.

Daga nan ne INEC ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu, 2023 domin gudanar da karashen zaben.

Amma lauyan dan takarar ya ce, a baya Kotun Koli ta yanke hukunci cewa duk batun da ke gaban kotun da ke da hurumin sauraron kara a kansa, to wajibi bangarorin da ke shari’ar su dakata har sai kotun ta yanke hukunci a kansa, ba tare da sun yi gaban kansu ba.