✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan takarar da ke hannun ’yan bindiga ya lashe zaben fid da gwanin PDP a Kaduna

An dai sace shi ne tun lokacin da mahara suka kai wa jirgin kasa hari

Dan Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Sadiq Ango Abdullahi, ya lashe zaben fid da gwanin dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Sabon Gari a Jihar Kaduna, duk da cewa har yanzu yana hannun ’yan bindiga.

An dai sace shi ne tun lokacin da mahara suka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari, sannan suka sace mutane da dama.

Sadiq dai ya sami kuri’a 28 yayin da sauran ’yan takarar suka biyo baya.

Sauran ’yan takarar, Hadiza Muhammad, da kuma Misis Paulina, Salisu Abdulhamud suka sha kaye a zaben.

Idan za a iya tunawa tun a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2022 ’yan bindigar suka yi awon gaba da shi da wasu matafiya a jirgin kasa.

Tun a lokacin ba a sake jin duriyarsa ba a fagen siyasan ba.

%d bloggers like this: