Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Idris a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Kebbi.
Jami’in hukumar mai kula da bayyana sakamakon zaben a Jihar, Farfesa Sa’idu Yusuf, ne ya bayyana sakamakon a Birnin Kebbi da yammacin Lahadi.
- Zaben Adamawa: Fintiri ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankali
- An kashe mutum 6 a zaben ranar Asabar a Kano
A cewar sa, Nasiru ya lashe zaben ne bayan ya sami kuri’a 409,225, inda ya doke abokin karawarsa na kurkusa, Janar Aminu Bande (mai ritaya) na PDP, wanda ya sami kuri’a 360,940
Idan za a iya tunawa, tun da farko dai an gudanar da zaben ne ranar 18 ga watan Fabrairu, amma INEC ta bayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba saboda aringizon kuri’u da rikici a wasu rumfunan.
Farfesa Sa’idu ya ce a yayin karashen zaben da aka gudanar ranar Asabar, adadin masu rajista a mazabun da aka yi zaben su ne 95,897, sai wadanda aka tantance kuma guda 40,186.
“Daga cikin wannan adadin, APC ta sami kuri’a 20,967, yayin da ita kuma PDP ta sami 17,960,” in ji shi.