Wani dan Majalisar Tarayya a Birtaniya ya sanar da sauka daga kujerarsa bayan samunsa da kallon bidiyon batsa a wayarsa ta salula yayin zama a zauren majalisar ta House of Commons.
Tun a Juma’ar makon jiya ce jam’iyyarsa ta Conservatives ta sanar da dakatar da Neil Parish bayan ya gabatar da kansa a gaban Kwamishinan Tabbatar da Ka’idodi na majalisar domin a dauki matakin da ya dace a kansa.
- An kai hare-haren ta’addanci fiye da dubu 5 cikin shekaru 3 a Yammacin Afrika
- Ta’addanci: Kungiyar Ansaru ta fara daukar mayaka a Kaduna
Mista Parish ya yi nadama kan laifin da ya aikata wanda ya ce ya faru ne karo biyu a lokuta daban-daban yayin zaman majalisar.
Cikin nadama Mista Parish ya ce gwara duk abin da zai faru ya faru amma ba zai iya ci gaba da kasancewa dan majalisa ba a sakamakon wannan abun kunya da ya aikata wanda kuma ya shafi iyalansa da mazabar da ya fito.
Mista Parish wanda manomi ne, ya ce ya kalli bidiyon batsar karon farko a bisa kuskure, wanda ya ce bai yi aune ba ya fara kallo a yayin da yake neman wasu motocin ayyukan gona da ke da suna makamancin na badala.
“Tabbas na tsaya na kalli bidiyon na wani dan lokaci wanda ko kadan bai kamata a ce na yi hakan ba.
“Sai dai kuma na sake aikata wannan laifi da gangan a karo na biyu yayin wani zama a zaure majalisa, kuma wannan abu da na aikata wauta ce tsagwaranta.
“Ko kadan bana alfahari da wannan laifi da na aikata, kuma ban yi nufin wadanda ke zama kusa da ni su gani ba.
“A yanzu babu abin da zan yi don na kare kaina, don tabbas abin da na aikata laifi na babba, ina tunanin rashin hankali ne ya rude ni a lokacin da na aikata hakan.