An samu wani dattijo mai shekaru 50 da ya yi wa wata karamar yarinya ’yar makotansa mai shekaru 6 fyade a Hayin Danmasani da ke unguwar Rigasa a Karamar Hukumar Kudancin Kaduna a jihar Kaduna.
Dagacin Hayin Danmasani, Umar Ibrahim ne ya tabbatarwa wakilin Aminiya faruwar lamarin a ranar Litinin.
- Kotu ta daure wanda ya lalata karamar yarinya shekara bakwai
- Lakcara da ’ya’yansa sun kubuta daga masu garkuwa
- Za mu ba ’yan kabilar Igbo kariya a Kano —Sarkin Bichi
Ibrahim ya ce yarinyar ta yi sa’a kwananta na gaba sakamakon iyayenta da suka yi gaggawar kai ta kai ta asibiti inda har aka yi mata aiki a al’aurar a dalilin afka mata da dattijon mai suna Ibrahim ya yi.
Dagacin ya ce, “Tabbas lamarin ya auku, kuma yanzu haka ana tuhumar wanda ake zargi da aikata laifin a Ofishin ’yan sanda na unguwar Rigasa.”
“Amma yau da safe sun bani labarin ana kokarin mayar da wanda ake zargi da laifin zuwa sashen binciken masu aikata miyagun laifuka na ofishin ’yan sandan (CID).
“Mutumin da ake zargi da aikata laifin yi wa yarinya mai shekaru 6 fyade yana da shekaru 50, mai iyali ne da yake da mata biyu kuma gidansa na makotaka da gidan iyayen yarinyar da aka yi wa fyaden.”
“Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a amma ’yan sanda sun shiga maganar a ranar Litinin kuma yanzu haka al’ummar yankin suna jiran sauraron matakin da za a dauka a kai.”
“Na sanar da ’yan sandan cewa, akwai rahoton da Asibiti suka bayar, yanzu haka suna kokarin mayar da lamarin zuwa ofishin binciken masu aikata miyaun laifuka.
“Mahaifiyar yarinyar ta damu matuka tana mai neman lallai ’yarta na bukatar a bi mata hakkinta.”
A yayin neman jin ta bakin jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sanda na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya bukaci a kara masa lokaci domin gudanar da zurfafa bincike a kan lamarin.