Wata Babbar Kotun Majistire da ke zaune a Kafanchan, ta ba da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 50 a gidan dan Kande bayan ya yi ikirarin yi wa diyar makwabcinsa cikin shege.
Sai dai Alkalin da ya jagoranci zaman kotun, Abdulaziz Ibrahim, ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Janairu domin ci gaba da shari’ar wanda ake zargi.
- Nuna tsiraici: Bidiyon sabuwar wakar Hausa ya ta da kura a intanet
- Rikicin Amurka: Za a fara kada kuri’ar tsige Trump
Mutumin da ake tuhuma mai suna Anthony Garba, ana zarginsa da aikata masha’a da saduwa ba tare da aure ba kamar yadda maihaifin yarinyar, Elkana Nache ya shigar da korafi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa laifin da ake tuhumar mutumin ya saba wa sashi na 186, 364 da 368 na kundin manyan laifuka na Jihar Kaduna.
Elkana wanda mazaunin unguwar Gidan Waya ne ya ce diyarsa ba ta dade da fara koyon gyaran gashi ba a shagon matar wanda ake zargi kuma a yanzu ya lalata mata tarbiya.
A cewarsa, lokacin da aka yi mata tambaya kan lamarin, ’yar ta shaida cewa gidan wanda ake zargi ne ta saba zuwa sharholiyarta kuma akwai wani karo daya da ya yi yunkurin yi mata fyade.