✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan shekara 15 ya kashe abokinsa a Kano

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin

Wani matashi mai shekara 15 ya soki abokinsa da wuka a yayin wata takaddama, wanda hakan ya zama ajlinsa.

Lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano a ranar Juma’a, inda matasan suka samu sabani a wajen wasan kwallon Sunuka.

A cewarsa, marigayin ne a lokacin takaddamar ya kalubalance shi da idan ya isa ya zo su je bayan gari domin a raba raini.

Shi kuma da ya tashi zuwa sai ya tafi da wukar da yake yankar rake.

“Muna zuwa sai ya shake ni, ya kama ni da duka, ni kuma da na ga haka, sai na fito da wukar na caka masa a kirji,” in ji shi.

An garzaya da Musbahu zuwa Asibitin Murtala na cikin birnin Kano, a inda suna zuwa, ko fita da shi daga mota ba a yi ba, da likita ya duba shi, ya ce ya mutu, in ji kawun marigayin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin.

 

Madogara: Rahama Radio