Mutum mafi tsufa da nisan shekaru a duniya, dan kasar Japan Hidekichi Miyazaki, ya ksalubalanci magujin duniya, Usain Bolt. Wannan tsoho dan shekara 104, ya taba samun kambin tserejn mita 100 da ya kammala cikin mintuna 29 da dakika 83, har ta kai ga an yi masa lakabi da sunan “Golden Bolt,” bisa la’akari da nasarar da mai rike da kambin gudun duniya dan kasar Jamaica, Usain Bolt ya samu.
Wannan tsoho ya sha alwashin yin gasar tsere da Bolt, inda ya bayyana sirrin nasarar gudunsa da wani sinadari na lemun zuma-zumar tanjirin (tangerine) da ’yarsa ke hadawa.
“Ina sha’awar yin gasar tsere da Bolt,” a cewar wannan tsoho mai furfurar gashin kai, a lokacin da yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, bayan ya kammala gudunsa a gasar wasannin kasar Japan da aka gudanar a Kyoto. “Ina kokarin ganin tabbatar mafarkina. Ina kokari wajen horar da jikina don kasancewa cikin koshin lafiya. Wannan kuwa shi ne abu mafi muhimmanci ga kowa,” inji shi.
Wannan dattijo an haife shi a shekarar 1910, shekarar da kasar Japan ta mamaye kasar Koriya, kuma a zamanin da aka kera jirgin ruwa Titanic. Miyazaki ya shawarci magujin duniya kan nau’in abincin da ya kamata ya rika ci, wanda ya samu nasarar cin gasar tserensa cikin mintuna tara da dakika 58. “Jikina dan siriri ne, don ina kula da abin da ya dace in rika ci,” a cewar Mityazaki, wanda tsawonsa bai wuce mita daya da rabi ba, sannan yana da nauyin kilo 42.
A kasa irin Japan da al’ummarta ke da tsawancin kwana, mutanen irin su Miyazaki sun zama tambarin tsufa da nisan shekaru. Kimanin ’yan fansho mutum dubu shida aka yi rajistarsu, wanda ke yin wasan tsere a tarayyar kasar, inda suke kewaya fili sau 40 a kowace shekara, a daukacin fadin kasar.
Lokacin da Miyazaki ya kammala zagaye na 38 da digo 35 cikin dakika 20, sai ya fado a hannun ’yarsa ’yar shekara 73, mai suna Kiyono, inda ya tsere wa abokin karawarsa Yoshio Kita; ya yi ta rera wakokin nasara.
dan shekara 104 ya kalubalanci Usain Bolt su yi gasar tsere
Mutum mafi tsufa da nisan shekaru a duniya, dan kasar Japan Hidekichi Miyazaki, ya ksalubalanci magujin duniya, Usain Bolt. Wannan tsoho dan shekara 104, ya…