Stephen, dan shahararren dan kwallon Green Eagles Segun Odegbami zai angwance.
A wata sanarwar da angon da kuma amaryar suka fitar a kafar sadarwarsu ta Twitter a ranar Talatar da ta wuce, sun bayyana auren zai gudana ne a ranar 14 ga watan Mayun 2016 a Amurka.
Stephen dai shi ne na biyu a cikin ’ya’yan da Segun Odegbami ya haifa. Kwanan nan ya kammala karatunsa a wata Jami’a da ke Amurka kuma ana kyautata zaton a can Amurka zai zauna da amaryar idan ya aureta.
Ita ma amaryar tasa wacce ba a ambaci sunanta ba, rahoton ya nuna a can Amurka take da zama. Hasalima a can suka hadu inda suka dade suna soyayya kafin su yanke shawarar yin aure a wannan shekara.
Idan za a iya tunawa, Segun Odegbami yana daga cikin zaratan ’yan kwallon Green Eagles kafin a sauya mata suna zuwa Super Eagles. A wancan lokaci ana yi masa kirari ne da “Mathematical” watau mai lissafi ganin yadda ya zama gwani wajen gudu da kwallo a kan layi ba tare da ta fita ba.
Bayan Segun Odegbami ya yi ritaya daga kwallo ne ya zama mai yin sharhi a kan al’amurran kwallo a kafofin watsa labarai ciki har da jaridar Daily Trust ta Turanci da ke fitowa a duk ranar Asabar (Daily Trust on Saturday).
dan Segun Odegbami zai angwance
Stephen, dan shahararren dan kwallon Green Eagles Segun Odegbami zai angwance. A wata sanarwar da angon da kuma amaryar suka fitar a kafar sadarwarsu ta…