Ana zargin wani dan sanda mai suna Sufeto Alpha Lamurde da dukan wata budurwa Bilkisu Ummi Isa, lamarin da har sai da ya kai ta ce ga garinku nan.
Lamarin ya faru ne a ofishin ’yan sanda da ke Calvary a garin Maraba da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.
Wata da ke tare da marigayiyar a lokacin da abin ya faru, Ruqayya Muhammad ta ce, “A gabana ya yi ta dukanta da bulala ya kuma buga kanta da bango har sai da ta suma. An kama mu ranar Litinin, Bilkisu ta yi jinyar kwana 6, ta rasu ranar Lahadi.”
Yayan marigayiyar, Zakariya Isa ya ce, “Abin da ya faru shi ne, wani tsohon saurayin marigayiyar ne da suka rabu fiye da shekara mai suna Abdul ake zargin ya sace katin cire kudi da kudi da ya kai fiye da Naira miliyan daya na wani maigidansa Jafar ya gudu.
- ’Yan sanda sun mayar da N3.9m ga iyalan wanda ya rasu a hatsarin mota
- ’Yan bindiga sun sako mai jego da manomi a Taraba
“Sai ’yan banga suka zo suka nemi Bilkisu ta je ofishin ’yan sanda don ta yi bayani. Amma sai Sufeton ya yi ta dukanta sai da babanmu ya je aka ba shi belinta.”
Ruqayya ta ce, “Jibrin ne da wani da ake kira Masta dan banga suka zo gidanmu suka ce ana nemana, don ni kawar Bilkisu ce. Da na bi su sai suka biya gidan su Bilkisu suka ce ana nemanta, wai za mu amsa tambayoyi.
“Da muka je sai suka ce wai ana neman Abdul don ya sace Naira miliyan daya amma Ummi ta fito da shi, sai ta ce ai sun fi shekara da batawa. Sai Sufeto Alpha Lamurde ya yi ta marinta da duka da gwara mata kai a bango.
“Ni kuma sai ya ce yana sona, ya ba ni lambarsa, ya ce in kira shi za mu hadu a otel, hakan ya sa ni bai buge ni ba.
“Da na ce masa ta suma sai ya debo ruwa ya kwara mata, sannan iyayenmu suka yi belinmu,” inji ta.
Malama Hadiza, mahaifiyar marigayiyar ta shaida wa Aminiya cewa, “Ina neman gwamnati da rundunar ’yan sanda da ’yan Najeriya su taimaka don ganin an gurfanar da dan sandan a gaban kotu don bin hakkin ’yata.”
Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel da farko ya ce ba su samu labari ba, sai daga baya ya ce, “Labarin ba haka ba ne, na tuntubi DPO na yankin ya ce abin ya faru ne a wajen sayar da mota a Maitama da ke Abuja, inda Abdul ya dauke katin cire kudi ya gudu zuwa Titin Calvary a Maraba Karu.
“An kama maragayiyar a gidan da Abdul yake boyewa inda aka gano katin da wasu kayayyaki.”
Ya ce sun samu rahoton abin da ake zargin dan sandan, sun kuma tuntubi iyayenta, inda suka ce dama ta dade ba ta da lafiya.
“Ba a kulle ta ko gana mata azaba ba,” inji ASP Ramhan Nansel.