✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya kashe amarya a zanga-zanga a Kano

A mako mai zuwa za a daura auren Firdausi kafin dan sandan ya harbe ta har lahira a ungwar Rijiyar Lemo

Wani dan sanda ya kashe wata amarya da ake shirin daurin aurenta a yayin zanga zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Jihar Kano.

Amarya Firdausi Muhammad wadda ake shirin aurenta ta rasu ne bayan wani dan sanda ya yi harbi a unguwar Rijiyar Lemo da ke Karamar Hukumar Fagge a yayin zanga-zangar.

Aminiya ta gano cewa a mako mai zuwa za a daura auren Firdausi kafin dan sandan ya aika ta barzahu.

Kisan masu zanga-zanga da ake zargin ’yan sanda sun yi a Jihar Kano sun auku ne a unguwannin Kofar Nassarawa, Kurnar Asabe da kuma Rjiyar Lemo.

A unguwar Kofar Nassawa ne aka wani mai suna Umar Abubakar Hausawa ya rasu sakamakon harbin da wani dan sanda ya yi a ranar a aka fara zanga-zangar.

Dan uwansa mai suna Rabiu Abubakar, ya ce: “A lokacin da Umar ya ji cewa kannenmu sun shiga cikin masu zanga-zangar abin ya bata masa rai, shi ne ya shaida wa mahafiyarmu cewa bari ya je ya sa su dawo. A can shi kuma ya gamu da ajalinsa.”

A Kofar Nassarawar dai an kashe wani mai suna Abdulkadir Labaran Babah Alfindiki, wanda mahaifiyarsa, Aisha Isah Babah, ta shaida wa wakilimu cewa “ya je wurin kasuwancinsa amma bai zo ya ci abincin rana ba, wanda hakan ya sa ni cikin damuwa.

“Amma ni ban kira shi a waya ba, shi ma kuma bai kira ni ba, kuma ban bayyana wa kowa damuwata ba. Ni ban sani ba ashe kashe shi aka yi.”

A cewarta, ta mika wa Allah komai game da marayan dan nata kuma ba za ta kai wa kowa kara ba.

Maryam Sani, mahaifiyar wani dan shekara 15, Kashifu Abdullahi Gyaranya, wanda aka kashe a lokacin zanga-zanar, ta ce: “zai fita daga gida na tambaye shi inda za shi, ya ce wurin abokansa za.

“Na gargade shi cewa kada ya shiga cikin zanga-zangar kuma ya ce min ba zai shiga ba, sai kawai daga baya aka kira ni a waya cewa an kashe shi. Shi ke nan.”

Amma da yake martani kan lamarin harbin masu zanga-zangar, kakakin ’yan sanda na jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ’yan sanda sun yi iya kokarinsu wajen tabbatar da doka da oda,  a unguwar Rijiyar Lemo, inda matasa suka yi kokarin fin karfinsu.

“Abin da ya faru shi ne gwamnatin Kano ta sa dokar hana fita, amma wasu daruruwan matasa suka fito suna kokarin fasa shagunan jama’a su sace kaya.

“Sakamakon haka jami’anmu suka yi kokari  watsa su koma gidajensu, amma sai yaran suka fara tarzoma suna jifan jamia’n mu”.

A cewar Kiyama, lamarin ya sa ’yan sanda suka nemi a kawo musu dauki da karin ma’aikaa, domin tabbatar da doka da oda a yankin na Rijiyar Lemo.

Jami’in ya bayyana cewa duk da cewa doka ta ba wa yan sanda damar kare kansu, amma  runduar ta fara gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru. 

Aminiya ta ruwaito yadda wani soja ya harbe wani dan sakandare, Isma’il Muhammad, a cikin gidansu a yankin Samaru da ke Zariya a Jihar Kaduna a yayin zanga-zangar gama-garin.

Kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin dan Adam dai sun yi kira da gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanarwa da hukunta duk wani jami’in tsaro da aka samu da laifin kisa a lokacin zanga-zangar.

Gamayyar kungiyoyin akalla su 13 sun bayyana cewa rashin hukunta jami’an da ke da laifi zai zama mummunar shaida a kan Gwamnatin Shugaban Bola Ahmed Tinubu da maganar da take na neman sulhu da masu zanga-zangar.

Sun kuma bayyana cewa kisan masu zanga-zangar da jami’an tsaro suka yi ba komai ba ne face kisan babu gaira babu dalili don haka wajibi ne a hukunta su domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasar.