Wasu jami’an ’yan sanda sun yi barazanar yin kasa-kasa da wakilin kamfanin Daily Trust masu buga jaridar Aminiya na Jihar Katsina, Malam Tijjani Ibrahim a lokacin da yake tsaka da gudanar da aikinsa.
’Yan sandan sashen CTU sun yi wa Malam Tijjani barazanar ce a lokacin da yake kokarin daukar hoton manyan bakin da suka halarci taron bude wani gidan marayu da makaranta wanda Sanata Sadik ’Yar’aduwa ya gina.
- Zaben Kano: ’Yan jagaliya sun yi awon gaba da kayan zabe
- Abubuwan da ya kamata ku sani game da yakin basasar Najeriya
- Mutane sun tsere yayin da sojoji da Boko Haram ke gwabza fada a Borno
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
Dan sandan na farko ya gargadi dan jaridar cewa kada ya kuskura ya dauki hoton, duk kuwa da tazarar da wakilin na Dailytrust ya bayar a lokacin da yake kokarin daukar hoton don kiyaye dokar ba da tazara a wajen taro.
Bayan Tijjani ya nuwa masa katinsa na shaidar aiki, kan ka ce kwabo sai wani dan sanda daga can gefe ya yunkuro ya bangaje dan jaridar; ya kuma yi kurarin zai yi kasa-kasa da shi a wurin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce suna bincike a kan lamarin.
Samun irin wannan barazanar ba bakon abu ba ne ga ’yan jarida daga jami’an tsaro.
A wasu lokutan ma har hana su gudanar da aikinsu ake yi, ko a kwace ko farfasa masu kayan aikin, ko ma a yi musu dukan tsiya.
Duk da cewa ’yan jarida kan hadu da irin wannan matsalar da jami’an sashen na CTU a wurare daban-daban, irin wannan furuci, musamman a Jihar Katsina inda ayyukan mahara suka yi kamari, kamata ya yi jami’in tsaron ya yi su ne a aikace yayin fuskantar ’yan bindiga, barayin shanu, da masu satar mutane ba wa a wajen taron da aka gayyato dan jaridar ya yi aikinsa ba.