✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan sanda mai shekara 91 ya sha alwashin ci gaba da aiki

Wani dan sanda mai shekara 91 mai suna LC “Buckshot” Smith, an kiyasta shi ne wanda ya fi kowane jami’in dan sanda dadewa a bakin…

Wani dan sanda mai shekara 91 mai suna LC “Buckshot” Smith, an kiyasta shi ne wanda ya fi kowane jami’in dan sanda dadewa a bakin aiki.

LC Smith ya ce bai da shirin yin ritaya, kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa jama’arsa hidima, inda yake aikin kwanaki hudu duk mako.

Buckshot ya kasance bai da kuzari kamar yadda ya kasance a baya ba  sakamakon tsufa da ya yi, amma duk da haka yana rangadi a hanyoyin garinsa da ke birnin Camden a Jihar Arkansas ta Amurka.

Ya yi shekara 46 yana aikin dan sanda, sannan ya yi ritaya amma duk da haka bai son ajiye aikinsa sama da watanni biyar da yin ritaya.

Ya kasance jami’in dan sandan da bai farautar masu laifi, sai dai shi abin da ya fi bukata shi ne, ya zama jami’in dan sanda kawai.

A lokacin da ya cika shekara 80 da haihuwa, sai ya koma da aikinsa a garinsu saboda yana sha’awar taimakon unguwarsu da shirin yin abu mai kyau ga al’ummar yankinsa.

Tun a watan Janairun shekarar 2011, bayan yin ritayarsa daga aiki, Smith ya fara tuna shekarun baya, wanda a yanzu ya yi shekara 10 yana aikinsa na dan sanda a yankinsa, ya kasance yana kaunar jama’ar unguwarsu, su ma suna kaunarsa.

A ranakun aikinsa, yana fara aikin ne daga karfe 7 na safe zuwa karfe 3 na rana a sashen masu gabatar da masu laifi gaban kotu.

A yankinsu yana taimakon jama’a wajen kiyaye ka’idojin hanya, yankunan da akwai makarantu, da yi wa masu fareti rakiya da dai sauransu.

A lokacin da Smith ya haura shekara 90, ya ci gaba da sanya kayan sarki na ’yan sanda rike da makami, duk da yake bai amfani da makamin.

Magajin garinsu mai suna Mayor Julian Lott ya yi ikirarin cewa, tsohon dan sandan ya mallaki makamai masu nagarta.

Mayor Lott ya ce: “Smith ya san mahaifiyar kowa da kakarsa a yankin, don haka yana da damar da zai iya magana a matsayin hukuma ga rayuwar jama’armu.”

Smith ya yarda cewa, ba wai rike bindiga ko nuna shaidar zama dan sanda ba ne ya sa ya zama jami’in dan sanda mai kishi, sai dai girmamawar da jama’a ke yi masa kuma yake musu.

Kasancewarsa mai tausayi, ya yi ikirarin taimakon jama’arsa ta hanyar fitar da mafi yawa daga gidan yari a maimakon garkame su, a karkashin kulawarsa.