Wani dalibi mai shekaru 25 da ke yi wa kasa hadimia Bright Martins Ekong, ya sadaukar da alawus dinsa na wata 10 domin biya wa wata yarinya mai shekaru 12, Sokari Wealth, kudin makarantar karatunta na sakandare gaba daya.
Ekong wanda dan asalin Jihar Akwa Ibom ne ya kamala karatunsa a Jami’ar Kalaba in a ya karanci fannin Chemistry, ya ce ya biya wa dalibar kudin makaranatar ne a matsayin tasa gudummawar ga al’ummarsa.
“Sokari na da kokari sosai, don haka na ga bukatar na karfafa mata gwiwa la’akari da marainiya ce, kuma mahaifiyarta ba ta da karfin da za ta biya mata, ka ga kyale ta hakan asarar basirarta zai zama,” in ji shi.
Wannan makaranta dai wacce a cikinta ne Ekong ke yi wa kasa hidima , na kauyen Bukuma da ke karamar hukumar Degema a jihar Rivers.
Ekong ya kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki fannin ilimin kasar nan da muhammanci ta hanyar ba wa makarantu wadataccen kudin gudanarwa, kasancewarsa jigon cigaban kowacce al’umma.
Mahaifiyar yarinyar, Madam Sokari, ta mika godiyarta ga Ekon bisa wannan tallafi da ya ba wa ’yar tata, kasancewar abu ne da ba ta taba tsammanin samu daga wani ba, kuma ya zo ne a daidai lokacin da take bukata.