Wani shahararren mai arziki a Najeriya mai suna Kunle Soname ya samu nasarar saye wani kulob a Fotugal bayan ya mallaki hannun jarin kashi 70 bisa 100 na kulob din a ranar Juma’ar da ta wuce.
Bayannin haka na kunshe ne a wata sanarwa da kulob din Clube Desportibo Freirense na Fotugal ya fitar a kafar sadarwarsa.
Sanarwar ta ce: A ranar Juma’a 9 ga watan Oktoban da muke ciki ne muka cimma matsaya wajen sayar da kashi 70 daga cikin 100 na hannun jarin kulob din Clube Desportibo Freirense ga attajiri dan Najeriya Kunle Soname kuma tuni kamfaninsa Trabistock Global Resources Limited ya kammala biyan kudin. Muna fata wannan yarjejeniya da muka kulla da Kunle Soname za ta kawo hadin kai da kuma cigaban kulob din”.
Shi dai kulob din ya taba yin wasa a gasar rukuni-rukuni na Fotugal a shekarar 2011 amma daga baya ya samu koma baya inda yanzu haka yake buga wasa a rukunin ’yan dagaji.
Wannan nasarar cinikin sayen wani kulob a Fotugal shi ne irinsa na farko da wani dan Najeriya ya taba yi a Fotugal. Kunle Soname dai shi ne mutumin da ya mallaki kulob din Remo Stars Football Club a Najeriya.
A tattaunawarsa da ’yan jarida jim kadan bayan an kammala kulla yarjejeniyar cinikin a Fotugal Kunle ya bayyana matukar farin cikinsa a kan yadda ya cika burinsa na mallakar wani kulob a Fotugal duk da kasancewarsa bakin fata da ya fito daga Najeriya.
Idan za a tuna, shahararren attariji Alhaji Aliko dangote ma yana da yakinin ganin ya mallaki kulob din Arsenal da ke Ingila nan ba da dadewa ba.
Dan Najeriya ya sayi wani kulob a Fotugal
Wani shahararren mai arziki a Najeriya mai suna Kunle Soname ya samu nasarar saye wani kulob a Fotugal bayan ya mallaki hannun jarin kashi 70…