Abdulmalik Ja’afar Mahmud, wanda ya kasance da ga marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, ya koma ga Mahallicinsa a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba na 2020 sakamon hatsarin mota.
Ministan Sadarwa, Sheikh Dokta Isa Ibrahim Ali Pantami, da Sheikh Abdullahi Umar Gadon Kaya da Sheikh Mansur Sokoto, sun sanar da hakan a shafukansu na Facebook inda kowanensu ya mika sakon ta’aziyya tare da yiwa mamacin addu’a.
- Buhari ya yi alhinin mutuwar ’yar uwar Fayose
- Ta’aziyya: Buhari ya kai wa iyalan Yar’adua ziyara a Kaduna
A sakon da Sheikh Pantami ya wallafa ya ce: Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raji’un!
“Na samu labarin rasuwar AbdulMalik, dan Shaykh Ja’afar Mahmud Adam (RH).”
“Ina mika ta’aziyya zuwa ga ’yan uwansa da iyayensa, kan Allah Ya jikansa, Ya jikan iyayenmu da sauran ’yan uwanmu, kuma Ya kyautata namu bayan na su,…”
“Wanda ya mutu, bai yi sauri ba, kuma mu da muke nan bamu dade ba, sai mun zo in sha Allah.”
Shi kuwa Sheikh Mansoor Sokoto wanda Farfesa ne a ilimin Hadisi, bayan dora hoton Marigayi AbdulMalik a shafinsa na Facebook, ya kuma rubuta sakon cewa, “Yanzu muke samun labarin mun rasa danmu AbdulMalik Jafar Mahmud Adam a cikin wani hatsarin mota.”
“Ya Allah ka yi masa gafara. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.”
Sheikh Gadon Kaya a nasa shafin na Facebook ya wallafa cewa; “Innalillahi wa inna ilaihiraji’un.”
“Abdulmalik Ja’afar Mahmud Adam ya su yanzu.”
Ya kuma rubuta cewa za a sanar da lokacin da za a yi masa jana’iza tare da bayyana masallacin Usman bn Affan da ke Kofar Gadon Kaya a birnin Kano a matsayin wurin da za a sallaci gawarsa.