✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisar Tarayya ya tsallake rijiya da baya a Zamfara

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gusau da Tsafe, Alhaji Ibrahim Shehu Gusau ya tsallake rijiya da baya a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da…

 Motar dan majalisar Ibrahim Shehu da ‘yan bangar siyasa suka yi wa rotse a Gusau.Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gusau da Tsafe, Alhaji Ibrahim Shehu Gusau ya tsallake rijiya da baya a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da wasu ’yan bangar siyasa da suka kai masa hari a Gusau.
’Yan bangar siyasar sun kai hari ne ga ayarin dan majalisar lokacin da ya isa Gusau domin halartar wani taron masu ruwa da tsaki kan tsammanin da ake yi masa na tsayawa takarar Gwamnan jihar a karkashin sabuwar Jam’iyyar APC.
Shaidu sun ce maharan sun lalata gilasan wasu motoci da suke cikin ayarin dan majalisar wanda ke hanyarsa ta zuwa wurin taron, sai dai kuma dan majalisar ya sha ba tare da ko kwarzane ba.
Aminiya ta samu labarin cewa dan majalisar ya samu mafaka a masaukin baki na Shugaban kasa da ke Gusau, yayin da maharani suka yi awon gaba da wasu kudinsa masu dimbin yawa daga motarsa.
Da yake bayani ga manema labarai bayan kai masa harin Alhaji Ibrahim Shehu Gusau ya ce, bai taba cewa zai tsaya takarar wani mukami ba a jihar.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce shugabannin jam’iyyar a jihar sun ce ya bayyana niyyyarsa ta tsayawa takarar Gwamna, kuma duk kokarin da shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki suka yi na ya hakura bai cimma nasara ba.
An ce dan majalisar ya je Gusau ne domin amsa gayyatar dattawa da wasu fitattun ’yan siyasa kafin aukuwar harin, wanda ya ce an shirya shi ne domin cin zarafinsa.
Shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomin Gusau da Tsafe Alhaji Shehu J. Muhd da Alhaji Kabiru Mande Tsafe wadanda su ne suka rubuta takardar gayyata ga Ibrahim shehu, sun ce sun gayyace shi ne kan wasu matsaloli da suka shafi mazabarsa ba kan wata takara kamar yadda ake yada jita-jita ba.
Sun ce sun gaya masa sun sauya wurin taron daga Gusau zuwa Tsafe, kuma kafin ya wuce Gusau sun tare shi don ya tsaya amma bai tsaya ba, kuma ba su masaniya kan abin da ya faru, sai daga baya.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar ya ci tura, inda wayoyin Kakakin ’Yan sandan Jihar ASP Lawal Abdullahi ta kasance a kashe har zuwa hada wannan rahoto.