Dan Majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Nasarawa ta tsakiya, Alhaji Suleiman Adamu, ya rasu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa dan majalisar ya rasu ne a daren Alhamis, 30 ga watan Afrilu, a asibitin gwamanti da ke garin Keffi bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
- Tsohon shugaban Majalisar jihar Jigawa ya rasu
- Shugaban Majalisar Jihar Edo ne ya kamu da Coronavirus
Dan majalisa mai wakiltar Udege/Loko, Alhaji Mohammed Okpoku ne ya fitar da sanarwar hakan ranar juma’a, yana cewa za a yi jana’izarsa da safiyar ranar juma’a, 1 ga watan Mayu.
Alhaji Sulaiman Adamu ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar.