Wani dan Majalisar Wakilan Amurka ya sanar da ajiye mukaminsa bayan samunsa da laifin zabga karya kan batun wani tallafin kudi na siyasa da ke da alaka da wani attajiri dan Najeriya.
BBC ya ruwaito cewa, Jeff Fortenberry dan jam’iyar Republican ya wakilci Jihar Nebraska tsawon shekara 17.
- Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon Shugaban APC na kasa
- ECOWAS ta yi barazanar sake kakaba wa Mali sabon takunkumi
A ranar Alhamis, masu taimaka wa alkali yanke hukunci na tarayya suka gano cewa, Jeff Fortenberry ya yi wa jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, karya kan karbar gudunmuwar dala dubu talatin daga wani babban atajiri dan Najeriya, Gilbert Chagoury, wanda kuma yake da asali da kasar Lebanon.
A Juma’ar da ta gabata ce Shugabar Majalisar, Nancy Pelosi da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kevin McCarthy suka bukaci Fortenberry da ya yi murabus.
Cikin wasikar da ya aike wa Majalisar a ranar Asabar, Mista Fortenberry ya ce murabus dinsa zai fara aiki ne daga ranar 31 na wannan watan Maris da muke ciki.
Haka kuma akwai yiwuwar zai shafe shekara 15 a gidan yari kuma idan haka ta tabbata a watan Yuli mai zuwa za a tasa keyarsa zuwa can.