✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan kwallon U-23 ya samu kulob a Beljiyam

dan kwallon U-23 ta Najeriya Kingsley Madu ya koma kulob din S.b. Waregem da ke Beljiyam.  A da dan kwallon yana buga wa kulob din …

dan kwallon U-23 ta Najeriya Kingsley Madu ya koma kulob din S.b. Waregem da ke Beljiyam.  A da dan kwallon yana buga wa kulob din  A.S. Trencin da ke Slobakiya ne.
Kingsley wanda yana daga cikin ’yan kwallon U-23 da suka halarci gasar Olamfik kuma suka samu nasarar lashe lambar yabo ta Tagulla (Bronze) ya sanya wa kulob din hannu ne a kwantaragin shekara uku.
“Muna sanar da ku cewa Kingsley Madu, dan shekara 20 daga Najeriya ya sanya wa kulob din mu hannu a kwantaragin shekara 3”, kamar yadda wata sanarwa da kulob din ya fitar a shafin sadarwarsa ta nuna.
 Kingsley yana daga cikin ’yan kwallon da sabon kocin Eagles Grenot Rohr ya gayyato wadanda za su fafata da kasar Tanzaniya a garin Uyo a gobe Asabar.