✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan kwallon Najeriya ya makale a Ajentina saboda rashin kudin jirgi

Wani dan wasan kwallon kafa dan Najeriya da ke wasa a kasar Ajentina mai suna Felid Orode ya makale a kasar saboda rashin kudin jirgi…

Wani dan wasan kwallon kafa dan Najeriya da ke wasa a kasar Ajentina mai suna Felid Orode ya makale a kasar saboda rashin kudin jirgi da zai dawo Najeriya. Halin da dan wasan ya shiga ya sanya abokan wasan kwallon kafarsa a Ajentina hada masa kudin jirgin domin ya samu ya dawo Najeriya.
dan wasan wanda ya shafe kimanin shekara biyar bai dawo gida saboda rashin kudin da zai shigo jirgi, ya fara buga wa kungiyar wasan kwallon kafa ta Sharks da ke Fatakwal kafin ya fita waje domin ci gaba da buga kwallon kafa a can.
Felid Orode ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta San Lorenzo da ke rukunin farko na kasar Ajentina, daga baya rashin sa’a ta sa suka tura shi kungiyar Nueba Chicago a matsayin aro, inda daga bisani ya koma kungiyar CAI da ke bugawa a rukuni na biyu. Daga nan kuma ya koma kungiyar Sportibo Barracas a da ke rukuni na hudu a Ajentina inda yake ci gaba da buga wasa har yanzu.
 dan wasan ya yi aure da wata ’yar asalin kasar Ajentina mai suna Yasmine kuma ta haifa masa ’ya’ya biyu, namiji mai suna Salbador da mace mai suna Simona.
dan wasan ya yi wa abokan wasansa godiya tare da nuna farin ciki kan taimakon da suka yi masa, inda ya ce yana matukar farin ciki jin cewa zai koma gida domin ya ga mahaifiyarsa, ita ma ta ji dadin ganinsa.