✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Malawi ya mutu a Fotugal saboda maleriya

Wani matashi dan kimanin shekara 18 dan asalin Malawi Abel Mwakilama ya rasu a Fotugal a karshen makon jiya saboda kamuwa da ya yi da…

Wani matashi dan kimanin shekara 18 dan asalin Malawi Abel Mwakilama ya rasu a Fotugal a karshen makon jiya saboda kamuwa da ya yi da cutar zazzabin cizon sauro (maleriya).

Matashin, wanda yana daga cikin hazikan ’yan kwallon Malawi ya rasu ne a lokacin da yake da shekara 18 kamar yadda kafar watsa labarai ta Malawi24 ta ruwaito.

A zantawar da aka yi da Manajan kulob din matashin, wato Sporting Clube Esmoriz, benancio Patrick ya ce ana kyautata zaton mamacin ya kamu da cutar maleriya ce a lokacin da ya koma kasar haihuwarsa Malawi kimanin makonni uku da suka wuce don buga Gasar neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afirka na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) a tsakanin Malawi da Swazilan. 

Manajan ya ce kafin marigayin ya bar Fotugal lafiyarsa lau, amma jim kadan bayan ya koma ne sai ya rika fadin yana jin matsanancin ciwon kai da hakan ta sa aka tura shi asibiti.  A asibiti ne Likita ya yi masa gwaje-gwajen da aka gano ya kamu ne da zazzabin cizon sauro.

“A ranar Juma’a ce matashin ya rasu a wani asibiti da ke Porto na kasar Fogutal”, inji manajan.

“A gaskiya mun kadu matuka game da yadda matashin ya mutu a wannan lokaci, inji Alfred Gunda, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Malawi.

A lokacinda yake shekara 17 Mwakilama ya zura kwallaye a raga sau 37 ga kulob din da ya fara yi wa kwallo a Malawi mai suna Chitipa United al’amarin da ya sa kulob din ya samu nasarar hayewa gasar firimiyar Malawi a shekarar 2017.

Daga baya ne ya koma kulob din Sporting Clube Esmoriz da ke Fotugal inda ya zura kwallaye bakwai a wasanni biyar da ya yi wa kulob din.  Ya taba yin kwallo a Faransa kafin ya zoma Fotugal, inda a Fotugal din ne rai ya yi halinsa.