✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kunar bakin wake ya tashi bam a Ebonyi

Mutane sun tarwatse wajen neman mafaka saboda fargabar abin ka iya zuwa ya dawo.

Wani mutum ya yi kunar bakin wake inda ya tarwatsa kansa da wata rigar bam da ke saye jikinsa a Karamar Hukumar Afipko ta Arewa da ke Jihar Ebonyi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, lamarin ya auku ne da misalin karfe 12.00 na ranar Talata yayin da mutum ya yi yukurin shiga wata Makarantar Firamare da zummar kai harin inda masu gadinta suka hana shi shiga.

Yankin da lamarin ya auku ya zama kufai a yayin da sawu ya dauke kuma duk mutane sun tarwatse wajen neman mafaka saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo.

A cewar majiyar rahoton, “Mutumin ya yi kokarin shiga Makarantar Firamare ta Amaizu/Amangballa, amma masu gadinta suka hana shi shiga bayan ya gaza bayyana musu dalilin ziyarar da ya kawo makarantar.

“Nan da nan ya fara gudu a cikin wani jeji da ke kusa da makarantar wanda zai tashin bam din aka ji mai karar gaske.

“Tuni mutanen yankin suka bazama domin tsira da lafiyarsu yayin da bam din ya tashi,” a cewar majiyar.

Ba a samu rahoton salwantar rai ko jikkata ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, haka kuma rundunar ’yan sandan jihar ba ta ce komai game da lamarin ba.

Sai dai Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Ebonyi, Stanley Okoro, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi wani karin bayani ba doriya a kan hakan.