✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan kokawa ya mutu a lokacin fafatawa

A ranar Asabar da ta gabata ne aka samu labarin mutuwar wani matashi wanda da ne ga wani shahararren dan kokawa a kasar Meziko. Matashin…

A ranar Asabar da ta gabata ne aka samu labarin mutuwar wani matashi wanda da ne ga wani shahararren dan kokawa a kasar Meziko.

Matashin mai suna Pedro Aguayo Ramirez, da aka fi sani da Hijo del Perro Aguayo, ya suma ne bayan da abokin karawarsa mai suna Oscar Gutierez ya sunkuce shi sama kuma ya maka shi a kan wata igiyiya a lokacin da suke gasar kokawa ta yankinsu. Da daya daga cikin ’yan kallo sun kadu a lokacin da suka kalli yadda al’amarin ya faru ta akwatin talabijin a wani gidan kallo da ke garin Tijjana na Meziko.
Alkalin wasan bay tsayar da wasan ba na tsawon minti amma da ya lura matashi Aguayo ya kasa tashi ne sai ya ja hankalin likitocin da ke duba lafiyar ’yan wasan, al’amarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti mafi kusa. Da misalin karfe 1 da rabi agogon kasar ce aka samu labarin rasuwar dan kokawar kamar yadda dan sandan da ke binciken al’amarin Raul Gutierrez ya sanar.
Shi ma daraktan da ke kula da yadda gasar ke gudana Joakuin Roldan, ya bayyana kadukarsa a kan faruwar al’amarin. “Ban san irin bayanin da zan yi ba a kan faruwar wannan mummunan al’amari, hasalima ban taba ganin tashin hankali irin wannan a daukacin rayuwata ba”, inji shi.
Tuni sashen binciken laifuffuka na rundunar ’yan sandan kasar ya fara bincike a kan musabbabin faruwar al’amarin.
Wannan dai shi ne karo na farko da wani dan kokawa ya mutu a lokacin da ake wasa a kasar Meziko.