✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Karya

Wani saurayi ne irin ’yan karyar nan, ya yi wa budurwarsa alkawarin zai ba ta kudi. Ya ce ta zo ta karba gobe. Ashe ba…

Wani saurayi ne irin ’yan karyar nan, ya yi wa budurwarsa alkawarin zai ba ta kudi. Ya ce ta zo ta karba gobe. Ashe ba da gaske yake ba, zolayarta yake. Bayan ta same shi da safe sai ya dauko katin ATM dinsa ya ba ta, ya ce ta je ta fitar da dukkan kudin  da ke ciki ya ba ta. Shi kuma ya san cewa babu komai a ciki. Bayan ta tafi da dadewa, sai saurayin ya ji an turo sakon tes a wayarsa. Yana budewa sai ya ga ashe wani abokinsa ne ya turo masa kudi, Naira dubu 80. Ba a jima ba sai ya kara jin an turo wani sakon, wanda ke cewa an cire Naira dubu 80 daga asusunsa na banki.
Daga Isah Ramin Hudu Hadeja, 08060353382