✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kamasho

Wani dan hayis ne idan ya je tashar mota, kullum aka loda masa fasonja, ba ya ba ’yan kamasho hasafi, kamar yadda sauran direbobi ke…

Wani dan hayis ne idan ya je tashar mota, kullum aka loda masa fasonja, ba ya ba ’yan kamasho hasafi, kamar yadda sauran direbobi ke yi. Wata rana ya cika motarsa da fasinja, har ma ya fara shirin tafiya, sai dan kamasho ya zo motar ya yi wa fasinjojin sallama, bayan sun amsa, sai ya ce musu: “Dama wani dan jawabi ne nake son yi maku, saboda duk abin da ya faru da ku a hanya, wajenmu za a dawo, don haka ina sanar da ku cewa direban motar nan yana da cutar farfadiya, don haka duk wanda ya ga zai amince ya hau, ruwansa, duk abin da ya faru kada a yi kuka da mu!” Rufe bakinsa ke da wuya sai fasinjoji suka yi ta fita daga motar, kafin ka ce wani abu, kowa ya kama gabansa,.