✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan Ibo: Mai kayar da Hausawa a kokawa ba guru ba laya

Aminiya ta samU tattaunawa da wani dan kabilar Ijaw daga jihar Bayelsa mai suna Ebikabowe Emmanuel Keku wanda ake yi masa lakabi da dan Ibo…

Aminiya ta samU tattaunawa da wani dan kabilar Ijaw daga jihar Bayelsa mai suna Ebikabowe Emmanuel Keku wanda ake yi masa lakabi da dan Ibo a gidan Kokawa na Freedom Theater da ke unguwar Agumalu a jihar Legas. dan Ibo ya yi fice a harkar kokawa a jihar Legas saboda irin yadda ya gagari fitattun ’yan kokawar gargajiya ta Hausawa na Legas. dan Ibo ya bayyana cewa iyawa da kwarewa su ne kan gaba ga duk wani siddabaru da mutum zai yi domin ya sami nasara a kokawa.

Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Ebikabowe Emmanuel Keku.Ni dan asalin Jihar Bayelsa ne. An haife ni kimanin shekaru 28 da suka gabata. Kuma na fito ne daga cikin kabilar Ijaw. Hausawa suna kirana dan Ibo a filin Kokawa. Na yi makarantar firamare da sakandire a jiharmu ta Bayelsa. Daga bisani sai na yanke shawarar zuwa Legas domin na nemi na kaina. Har gashi Allah ya sa ina da abinci a cikin harkar kokawa kuma ina yin ta ina samun ‘yan kudi.
Me ya sa ka yanke shawarar shiga wasan kokawar gargajiya ta Hausawa?
Dalili shi ne ita harkar kokawa ba ta takaita kawai ga al’ummar Hausawa ba. Mu ma a garinmu na Bayelsa muna yin kokawar gargajiya kuma muna gasa da ita, sai dai kawai akwai dan bambanci dan kadan tsakanin tamu da ta Hausawa. Ni da ma na iya kokawa tun ina karami, to da na zo Legas sai na sami labarin cewa Hausawa suna yin kokawa a nan Legas, sai na nemi wurin na zo na shiga kamar yadda kowa yake shiga. Ga shi yanzu na zama gwarzo a cikinta har kowa yana tsoron karawa da ni.
Shin yaya kake mu’amala da Hausawa duk da cewa ba ka jin yarensu?
Gaskiya ba na samun wata matsala da su duk da ba na jin Hausa nakan yi magana da su da Turanci. Ka san shi malam Bahaushe mutum ne mai saukin kai da son zaman lafiya kuma mutum ne mai son taimakawa jama’a. Shi ya sa ba na samun matsala da su kuma ina jin dadin yadda suke mu’amala da ni. Suna yi min barkwanci da raha. Gaskiya ina jin dadin mu’amala da su da kuma yadda suke yin kokawarsu ta gargaji cikin tsari da dokoki da ladabi da biyayya. Kuma wani abinda yake ba ni sha’awa shi ne idan mutum ya yi nasara sai a rika ba shi kudi tare da wanda ya kayar ba tare da nuna bambanci ba.
Me ya sa suke kiranka dan Ibo?
Ka san mafi yawan Hausawa sun dauka duk wanda ya fito daga yankin Kudu maso kudu wato South-South Ibo ne wanda ba haka ba ne. Akwai kabilu da yawa wadanda suke yarurruka daban-daban. Akwai kabilar Ijawa da Ikwere da Ishekiri da Ibibio da sauransu dukkan su ba Ibo ba ne kuma ba sa jin yaren Ibo.
An ce daukacin ’yan kokowar suna tsoron yin kokawa da kai saboda tsoron kada ka ba su kunya, me ye sirrin haka?
Gaskiya duk wani dan kokawa a nan gidan da jihar Legas baki daya yana tsoron karawa da ni saboda tsoron kada na kada shi. Domin babu wani dan kokawa da ban yi masa kayin wulakanci ba a nan gidan. Babu wani tsafi ko siddabaru, kawai kwarewa ce da iyawa da juriya da kuma dabara. Idan ka hada wadannan abubuwa ka gama da duk wani dan kokawa.
Shin ba ka tsoron guraye da layu da siddabarun da ’yan kokawa suke yi?
Ba na tsoron su kuma ba na shakkar abubuwan da suke daurawa. Ai idan ba ka iya ba babu yadda za a yi wani tsafi ko siddaru ya taimake ka. Iyawarka ce kawai za ta taimake ka ba wani siddabaru ba. Kawai ni na mika al’amarina ga Allah kawai. A wurinmu mu ba ma daura komai kuma ba ma wani siddabaru idan za mu yi kokawa. Muna yin amfani da karfi da iyawa ne kawai. Saboda haka ni ba na jin tsoron duk wani abinda mutum zai daura a jikinsa. Dabarar da nake yi shi ne idan na lura mutum ya yi siddabaru na kasa kayar da shi cikin lokaci, sai na wanke jikina da ruwa. Ka ga koda ya shafa mini wani abu ba zai yi aiki ba tunda na wanke maganin da ruwa. Sai ka ga da mun koma fili sai kawai na sami nasara a kansa.
Nawa kake samu a kullum?
Kudin ba shi da yawa. Ni ba kudin ne a gabana ba, kwarewa da karin ilimi ne a gabana. Domin idan kullum ka na kokawa da mutane daban-daban za ka rika samun darasi iri-iri. Wannan shi zai taimaka maka ka kasaita ka bunkasa kwarewarka. Saboda sha’awar da nake da ita shi ya sa na zo nan.
Me kake so ka cimma a kokawa?
Burina shi ne ina so na yi fice a duniya kowa ya san ni har ta kai na wakilci Najeriya a gasar kokawa ta duniya. Ban damu ba da halin da nake ciki a yanzu amma na san da yardar Allah mutane za su san ni nan gaba.