Umar, dan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya samu tikitin tsayawa takarar dan Majalisar Wakilai na Jam’iyyar APC a zaben 2023.
Umar Ganduje na neman wakilcin al’ummar Tofa da Rimin Gado da Dawakin Tofa a Majalisar Tarayya karkashin tutar APC.
- Jonathan zai iya sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023 — Kotu
- 2023: Tsohon Babban Hafsan Sojin Sama ne zai yi wa APC takarar Gwamna a Bauchi
Aminiya ta gano cewa, abokin takarar Umar Ganduje a zaben fidda gwanin, Junaidu Yakubu, ya janye mishi ne ana gab da zaben.
Janyewar ta biyo bayan zaman da masu ruwa-da-tsaki da kuma dattawan jam’iyyar a Jihar Kano suka yi ne ranar Alhamis karkashin jagorancin Sanata Barau Jibrin.
Haka shi ma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ya zama dan takarar gwamna na APC a jihar bayan da shige gaban abokin karawarsa, Sha’aban Ibrahim Sharada da yawan kuri’u.
Zaben ya kammala ne da kuri’u 2,420, inda daga ciki aka samu kuri’u marasa kyau guda 20.
Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’i zaben, Sanata Tijjani Yahaya Kaura, ya ce Nasir Yusuf Gawuna ya samu tikitin takarar ne da kuri’u 2,289 yayin da abokin kararwarsa, Sha’aban Ibrahim Sharada ya samu kuri’u 30.
Sai dai, Sha’aban Sharada ya ce bai gamsu ba da sakamakon zaben ba, don haka ya kai korafinsa ga Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC).