dan fim din Amurka, marigayi Paul Walker, ya bar wa diyarsa, Meadow dukiyar da aka kiyasta ta kai darajar Dala miliyan 25 (kimanin sama da Naira biliyan hudu), kamar yadda takardun wasiccin da ya bari suka nuna a kotu.
Kamar yadda takardun suka nuna, Meadow ’yar shekara 15 da haihuwa za ta gaji dukiyar ce a karkashin kulawar kakanta, mahaifin Paul; da kakarta, Cheryl. Takardun ba su ambaci sunan mahaifiyar yarinyar mai suna Rebecca ba, duk kuwa da cewa tana zaune da ita ne a birnin Hawaii.
Shi dai marigayi Paul Walker, wanda dan fim ne kuma mai tseren mota ya mutu ne yana dan shekara 40, a sanadiyyar hadarin mota a garin balencia da ke California-Amurka a watan Nuwambar bara. Shi kansa direban motar, wanda abokinsa ne, mai suna Roger Rodas ya mutu a hadarin.
dan fim Paul Walker ya bar wa diyarsa Dala miliyan 25
dan fim din Amurka, marigayi Paul Walker, ya bar wa diyarsa, Meadow dukiyar da aka kiyasta ta kai darajar Dala miliyan 25 (kimanin sama da…
