Mutane na ci gaba da bayyana gamsuwarsu matuka gaya da cika kwanaki 100 a kan mulki da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi, tare da bayyana irin nasarorin da suka ce an samu da kuma sauyi da aka samu idan aka kwatanta shi da shekaru 16 da jam’iyyar da ta sauka a mulki ta yi. Bayan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a fadin kasa baki daya da kuma matakan tsaro kwakkwara da wannan gwamnati ta dauka duka sun isa a yaba a nuna farin ciki, kamar yadda Alhaji Malami Ibrahim kofar Atiku ya bayyana a zantawarsa da Aminiya.
“A matsayina na dan kasuwa kuma tsohon ma’aikacin Gwamnatin Tarayya, ina matukar farin ciki da cikar kwanaki dari da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi a kan mulki, domin na ga ci gaba da dama. A sashen man fetur, a matsayina na talaka na ga an samu ci gaba matuka.” Inji shi.
Tsohon ma’aikacin ya kara da cewa yanzu suna sayen man fetur ko wace lita a kan Naira 87, wanda ya ce sun yi shekaru ba su samu wannan garabasar ba sai fa da wannan gwamnati Allah Ya kawo ta.
Ta fuskar masu karbar kudin fensho kuwa ya ce a matsayinsa na mai karbar fensho, tun daga hawan gwamnati sabuwa suka ga canji, ana biyansu kudinsu a kan lokaci har ma kari suka gani an yi masu na kudin bisa kan abun da ake biyansu da can.
Da ya juya kan harkokin kasuwanci, wanda halin yanzu shi yake yi, ya nemi Shugaban kasa ya dauki matakan tsaro tare da hukunta jami’an tsaron da ke kafa shingaye da na masu karbar haraji na babu gaira babu dalili, tun daga jihohin Arewa, idan sun dauko albasa zuwa kasuwannin jihohin Kudu don su sayar. “Haka ake tare mu, kowane shingen tsaro da na masu karbar rabano. Ina kira ga Shugaban kasa, ko ba a soke shi ba, a yi mana sassauci saboda yanzu idan muka dauko kaya daga Arewa za mu kai Kudu, sai mun kashe kudi wajen Naira dubu 30 a hanya, kafin kayanmu su isa can.” Ya bayyana lamarin da cewa wannan gasa masu aya a hannu ne ake yi a kan hanyoyin, tun daga Arewa zuwa Kudancin kasar nan.
dan fansho ya bayyana gamsuwa da canjin yanayi a Najeriya
Mutane na ci gaba da bayyana gamsuwarsu matuka gaya da cika kwanaki 100 a kan mulki da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi, tare da…