✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan damfarar Intanet ya kashe budurwarsa don yin tsafi da ita

Matashin ya tsere bayan kashen budurwa tasa.

Wani matashi a Jihar Edo da ake zargi da laifin aikata damfara ta Intanet ya kashe budurwarsa don yin tsafi da ita.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Egor da ke Jihar, a ranar 24 ga watan Disamban 2021.

Bincike ya gano cewar matashin bai jima da dawowa Najeriya daga kasar Ghana ba, sannan daga bisani ya kashe budurwar tasa don yin tsafi da ita.

Matashin ya fita yawo da budurwar, amma daga bisani aka tsinci gawarta a gefen hanya, an yankan mata wuya sannan matashin ya tsere.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da yadda lamarin ya faru.

Amma wani bidiyo ya karade kafafen sada zumunta, wanda ya yi nuni da yadda aka tsinci gawar yarinyar.

Ko da wakilinmu ya tuntubi kakakin ‘yan sandan Jihar Edo, Kontongs Bello, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana kokarin ganin matashin ya shiga hannu.

Ya ce mahaifin matashiyar ne ya shigar da kara kan lamarin, wanda tuni ‘yan sanda suka shiga bincike.