’Yan sanda sun cafke daya daga cikin ’yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Kwalejin Gwandun Daji ta Tarayya da ke Akfaka, a Jihar Kaduna.
Aminiya ta gano mutumin na daga cikin wadanda suka shirya suka kuma kai hare-hare hudu a makarantu a Jihar Kaduna, ciki har da kwalejin gandun dajin da aka sace dalibai 37 a watan Maris.
- Kotu ta sa a yi wa Sheikh Abduljabbar gwajin kwakwalwa
- Daukar makami don kare kai laifi ne —Babban Hafsan Soji
Bayan kwana 55 aka sako daliban bayan iyayensu sun biya kudin fansa Naira miliyan 15.
Majiyoyi sun ce an cafke dan bindigar ne a unguwar Asikolaye da ke garin Kaduna bayan ’yan sanda sun shafe makonni suna bibiyar sa.
Wani dan unguwar ya ce kusan wata biyu ke nan da mutumin ya dawo unguwar da zama, inda ya kama hayan gida, cewa zai ’ya’yan matarsa a makarantar Islamiyya.
A cewarsa, jami’an tsaro na tsare da mutumin da matarsa, kuma sun yi wa shugabannin al’umma a unguwar tambayoyi kafin daga baya suka saki shugabannin al’ummar.
Ya kashe mijinta ya aureta
Wani mazaunin unguwar ya shaida mana cewa ’yan bindiga ne suka kashe tsohon mijin matar wanda ake zargin, amma ba ta san cewa sabon mijin nata dan bindiga ba ne kuma yana da hannu a harin da aka kashe mahaifinta da tsohon mijinta.
“Bayan ya kashe mijinta, sai ya dawo ya aure ta ya kuma rike ’ya’yanta wadanda ba shekarunsu ba su wuce bakwai ba.
“Ita duk ba ta san abin da ke faruwa ba sai bayan da ya shiga hannu, ya kuma fallasa irin abubuwan da ya aikata a baya.
“Ya tabbatar wa ’yan sanda cewa yana cikin wadanda suka yi garkuwa da dalibai a makarantu da dama, ciki har da Daliban Afaka,” inji shi.
Sabon zuwa
Wakiliyarmu ta ziyarci unguwar, inda ta samu gidan da wanda ake zargin ya kama haya a Layin Dahiru Bauchi a kulle.
Wani makwabcinsa da ya ce suna magana ya ce wanda ake zargin ya ce musu shi dan asalin Ilorin, Jihar Kwara, ne, ya dawo da iyalansa Kaduna ne don ya sa su a makaranta.
“Ya ce mana sunansa Abubakar, amma ba mu san ko sunansa na gaskiya ba ne, wani tela ne a Badarawa ya hada mu da shi.
“Amma telan ya ce wa ’yan sanda cewa shi kaya kawai wanda ake zargin ke kawo masa dinki amma bai san cewa dan bindiga ba ne.”
Kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce suna gudanar da bincike kan lamarin, sai dai bai yi karin bayani ba.