Rishi Sunak, dan asalin kasar Indiya, na kan hanyarsa ta zama Firai Ministan Britaniya.
Rishi shi ne mutum na farko wanda ba dan asalin kasar Birtaniya ba da zai rike wannan mukami.
- Mahaifin Fira Ministan Burtaniya na neman izinin zama dan kasar Faransa
- Liz Truss: Abun da ya ci kujerar Fira Ministar Birtaniya a kwana 45
Dan majalisar dokokin Britaniya a karkashin jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Konzabatif, a yanzu haka ya lashe zaben zama shugaban ta, yana kuma kan hanyar zama a shugaban Britaniya.
Hakan ya biyo bayan makonni na fadi-tashi a majalisar na neman goyon baya, a inda abokan takararsa Penny Morduant da Boris Jonhnson suka gaza samun kuri’u a majalisar.
Idan hakan ta tabbata, wannan zai sa ya zama firai ministan kasar na uku a cikin watanni biyu, bayan saukar Borin Jonhson da kuma Liz Truss.
An haifi Sunak a shekarar 1980 a Southampton da ke Gabar Tekun Ingila, bayan da iyayensa suka yi gudun hijira a zuwa Birtaniya a shekarun 1960.
Ya zama dan majalisa ne a shekarar 2015 a karkashin a jam’iyyar Kosabatif masu ra’ayin rikau.