✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan aiki ya yi wa tagwayen mai gidansa fyade

Wata uwar ‘yan biyu ta zargi yaron aikin ta da lalata da ‘ya’yanta tagwaye masu shekaru 12. Dan aikin mai shekaru 26 ya ce tun…

Wata uwar ‘yan biyu ta zargi yaron aikin ta da lalata da ‘ya’yanta tagwaye masu shekaru 12.

Dan aikin mai shekaru 26 ya ce tun a shekarar da ta gabata yake yin lalata da ‘yan biyun idan uwarsu ta tafi aiki.

Uwar tagwayen ta ce bayan ta gano yana lalata da yaran ne ta yi karar sa a wurin ‘yan sandan Aguda a jihar Legas wadanda suka kama shi.

Kakakin rundunar ‘Yan Sanda Jihar Legas, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa wanda ake zargin ya amsa cewa a shekarar 2019 ya fara lalata da yaran.

“Kwamishinan ‘yan sandan Legas CP Hakeem Odumosu ya ba da umarnin bincike sannan a gurfanar da wanda ake zargi a kotu.

“Ya kuma gargadi iyaye da su kula da ‘ya’yansu sannan su rika sanin irin mutanen da za su ba wa amanarsu”, inji shi.

Ya ce rundunar ta dukufa wajen gano masu yi wa kananan yara fyade da cin zarafinsu tare da gurfanar da su a kotu domin su girbi laifin da suka shuka.