Ruwan sama na farko na 2023 ya sauka a yankin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jema’a a Jihar Kaduna a yammacin Lahadi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa an fara ruwan saman ne da misalin karfe 6:00 na yamma, wanda ya dauki sama sa awa guda ana yin sa.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’yan Najeriya suka karbi karin wa’adin tsoffin kudade
- Bayan kwan-gaba-kwan-baya, Buhari zai kaddamar da aiki 8 a Kano
Wasu mazauna yankin sun ce ruwan saman zai rage zafin da ake fuskanta a ’yan kwanakin nan a yankin.
Jesse Dakat, wani mazaunin garin, ya ce ruwan saman na farko alama ce ta albarka.
“Ruwan farko abin farin ciki ne idan aka yi la’akari da yanayin zafi da ake ciki na tsawon wasu kwanaki; ruwan saman ranar Lahadi ya samar mana kwanciyar hankali,” in ji shi.
Ya kara da cewa samun ruwan sama da wuri wata alama ce ta za a samu kyawawan abubuwa a gaba.
Shi ma wani mazaunin garin Walter Adamu, ya ce damina ta fara yin kira ne ga manoma da su gaggauta share gonakinsu don shirye-shiryen sabuwar shekarar noma.
“Ina ganin wannan alama ce ga manoma don su fara shirye-shiryen soma nona,” in ji shi.
Adamu ya roki Gwamnatin Jihar Kaduna da ta tallafa wa manoman jihar domin ganin an samu girbi mai kyau.