Kotu ta aike da wani darakta a Gwamnatin Jihar Sakkwato zuwa gidan yari saboda damfarar wasu masu neman aiki Naira milian 1.3.
- NAJERIYA A YAU: Shin Rikicin Manyan Jam’iyyu Zai Amfani Masu Tasowa A Zaben 2023?
- Cutar Kwalara ta kashe mutum 50 a Yobe
Lauyan EFCC, Hannafi Sa’ad, ya shaida wa kotun cewa, Hassan, wanda shi ne Darakan Gudanarwa a hukumarsa, ya karbi karbi kudade daga wasu mutum uku bisa alkawarin ba su aiki a gaban wani mai suna Dahiru Muhammad a matsayin shaida.
Lauyan ya ce wanda ake zargin ya kuma bai wa Aliyu Adamu-Tsaki, Yusuf Abubakar da Yahaya Salihu takardun daukar aiki na bogi, a watan Agustan 2021.
Daga baya ne aka gano cewa takardun daukar aikin da ya ba su na jabu ne, hasali ma hukumarsa ba ta dauki sabbin ma’aikata ba.
Lauyan mai kare wanda ake zargi, Aminu Mustapha, ya bukaci a bayar da belinsa, amma lauyan EFCC ya kalubalanci hakan, yana mai cewa zai bukaci karin lokaci domin yin nazari kan lamarin.
Sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba mai kamawa domin sauraron bukatar belin wanda ake tuhuma.