Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta gargadi ’yan Najeriya kan yadda wasu ’yan damfara ke amfani da sunanta wajen tallata bukatar neman daukar matasa aiki.
Kwamishinan INEC na kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Ilimi na Masu Zabe (IVEC), Festus Okoye ne ya bada sanarwar a ranar Asabar a Abuja.
- Kotu ta daure masu kwacen waya shekara 7 a kurkuku
- An ware biliyan 4 don zuba mai a motocin ’yan sanda
A cewarsa, wadannan ’yan damfarar suna amfani da kafafen sada zumunta wajen yada wani tsohon tallar neman daukar ma’aikata da hukumar tun da dadewa.
Ya ja hankalin matasa da cewa wadannan ’yan damfarar ba su da wata manufa face yi wa jama’a zamba cikin aminci.
Okoye ya ce “Hukumar ba tare da wata tantama ba ta nisanta kanta daga wadannan ’yan damfara sannan ta sake nanata cewa ta rufe shafin daukar ma’aikata tun lokacin da hukumar ta dakatar da aikin daukar ma’aikata,” in ji Okoye.
Ya tunatar da cewa hukumar a ranar 30 ga Mayu 2020 da 31 ga Disamba 2020, ta fitar da wata sanarwa da ke jan hankalin jama’a kan yada sanarwa kan yadda zargin ya samo asali.
“Muna sanar da jama’a cewa an dakatar da daukar ma’aikata.
“Hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin tsari mai kyau da nuna gaskiya.
“Duk lokacin da za a dauki aiki za a sanar da mutane ta hanyoyin da ya dace.
Ya kara da cewa “Muna bada shawara ga jama’a da su yi watsi da duk jita-jitar daukar ma’aikata da hukumar ke yi a matsayin ayyukan wasu bata-gari, wanda ke son damfarar mutane.”