✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambazau bai halarci taron Majalisar Zartarwa ba

Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau bai halarci taron Majalisar Zantarwa ba wanda ke wakana yanzu hakan. An fara taron ne da misalin karfe 11…

Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau bai halarci taron Majalisar Zantarwa ba wanda ke wakana yanzu hakan.

An fara taron ne da misalin karfe 11 na safe karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Amma har lokacin da ake hada wannan rahoton, Dambazau bai shigo zauren taron ba. Amma Shugabar Ma’aikata, Winifred Oya-Ita da Ministan Shara’a Abubakar Malami sun samu halartar taron.

Idan ba a manta ba dai, an kira sunayen Dambazau, Malami da Winifred ne ake cikin badakalar yadda aka dawo da Maina aiki, har aka tura shi ma’aikatar ta Dambazau. Lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, wanda har shugaban kasa ya salami Maina nan take, sannan ya bada umarni a bincika masa yadda aka yi har aka dawo da Maina duk da cewa EFCC na nemansa ruwa-a-jallo.