- Hukumar NCC za ta hada gwiwa da Kamfanin NSPM
Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya yaba wa kokarin hukumar na sanya ido kan harkokin sadarwa inda ya ce yanzu yana kokarin kafa tarihi dangane da yabon da hukumarsa ta samu daga Hukumar Yi Wa Aikin Gwamnati Garambawul (BPSR) shekara biyu da suka gabata.
Dambatta ya bayyana haka ne a Abuja yayin da ya karbi bakuncin Manajan Daraktan Kamfanin Buga Takardun Kudi da Muhimman Takardu na Kasa, Alhaji Abbas Umar Masanawa wanda ya ziyarce shi a ofishinsa.
Farfesan Injiniyan Sadarwar ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda a yanzu Hukumar NCC ta zama abar alfahari a duniya inda hakan ya sanya ta cimma nasarar a muhimman ayyukanta.
“Sakamako ya bayyana dangane da kokarin da hukumar ta yi na cimma matsayin fitacciyar hukumar sanya ido a duniya. Ba mu ne muka bai wa kanmu sakamakon ba, amma abu ne na aiki tukuru da sadaukar da kai na shugabanni da daukacin ma’aikatan wannan hukuma sannan muka cimma wannan matsayi a yau,” inji shi.
Farfesa Dambatta ya nanata cewa duk da nasarar da hukumar ta samu ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kara zage damtse don yin kari a kan nasarar da hukumar ta samu.
Tun farko, Shugaban Kamfanin NSPM ya bayyana cewa ya ziyarci hedikwatar hukumar ce don neman hadin gwiwa musamman a bangaren dab’in takardu masu muhimmanci.
Masanawa wanda manyan ma’aikatan kamfanin suka rufa masa baya, ya ce kamar Hukumar NCC, kamfaninsa yana son zama kamfani na duniya wanda zai janyo harkokin kasuwanci daga wajen kasar nan.