Iyayen marigayiya Hanifa, dalibar da malaminta, Abdulmalik Tanko, ya kashe bayan ya yi garkuwa da ita sun ce dama ba su taba shakku kan yi musu adalci a kotu ba.
Sun bayyana hakan ne a zantawarsu da Aminiya, jim kadan bayan alkalin babbar Kotun Jihar Kano, Mai Shari’a Mai Shari’a Usman Na’abba ya yanke wa Abdulmalik din hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin yin garkuwa da Hanifa da kuma kasheta.
- Kisan Hanifa: Kotu ta daure budurwar Abdulmalik Tanko shekara 2
- Hanifa: An yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa
Mahaifin yarinyar, Abubakar Abdulsalam ya ce “Dama ba mu taba tunanin ba za a yi mana adalci ba, Allah Ya tabbatar an yi adalci kuma muna godiya ga mutanen da suka zo nan, Allah ya muku albarka Allah mayar da kowa gida lafiya.”
Har wa yau, mahaifiyar yarinyar da aka yi kokarin zantawa babu abin ta ce sai Alhamdulillah, ma’ana sun gode Allah bisa adalcin da aka yi masu.
Yayin yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Usman Na’abba, ya ce kotun ta yanke wannan hukunci ne bisa gamsuwa da shaidu da hujjoji da masu gabatar da kara suka gabatar a gabanta.
Har wa yau, kotun ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin daurin shekara biyar saboda samunsa da laifin hada baki da kuma boye ta.