Wani babban malamin jami’a kuma kwararren manazarci a fannin sharhi kan jagoranci, Dokta Ahmed Adamu, ya ce manufar da ta sanya ake yawaita kai hare-hare makarantu tare da sace dalibai ita ce yunkurin da ’yan daban daji ke yi na samun shigar janyo hankalin gwamnati da kuma tattauna wa da ita.
A cewarsa, matukar gwamnati za ta yi ruwa da tsaki a lamarin garkuwa da dalibai, to kuwa babu shakka ’yan daban daji za su fi samun alheri wajen karbar kudin fansa.
- Messi ya sake kafa sabon tahiri a Barcelona da gasar La Liga
- Yadda Mata Ke Neman Kawo Karshen Kashe-Kashe a Zangon Kataf
“A yayin da gwamnati za ta rika sanya hannunta a cikin lamarinsu, suna ganin cewa yawan alherin da za su samu zai karu kuma hakan ya sanya suke ci gaba da daukar makamai domin ci gaba da cin karensu babu babbaka.”
“Sun ga abin da ya faru a baya lokacin da aka sace ’yan matan Chibok wanda ya dauki hankalin duniya baki daya. Kuma sun san cewa idan suna son kulawa makamanciyar wannan, dole ne su rika farautar makarantu suna sace dalibai wanda hakan zai basu damar mu’amala kai tsaye da gwamnati,” a cewar Dokta Ahmed wanda malami ne a jami’ar Nile da ke birnin Abuja.
Ya ce ’yan daban dajin sun fahimci cewa ta hanyar satar daidaikun mutane gwamnati ba za ta waiwaye su ba kuma galibi mutanen da suka yi garkuwa da su suna biyan kudin fansarsu ba tare da gwamnati ta yi wani ruwa da tsaki a kai ba.
Ya bayyana cewa abu ne mai sauki wadannan ’yan ta’adda su kai farmaki makarantu saboda babu wani tsaro a cikinsu kuma hakan yana kara basu damar sace mutane rigis a lokaci guda wanda daga bisani za su yi amfani da su a matsayin garkuwa ta harin dakarun soji.
“Wannan shi ne dalilin da ya sanya ’yan ta’adda ke barazanar kashe wadanda suka yi garkuwa da su a yayin da duk wani jami’in tsaro ya rabe su. Saboda haka duk lokacin da aka ce an yi garkuwa da mutane da dama, gwamnati ba za ta yi duk wata mai yiwuwa wajen ganin wadanda aka yi garkuwa da su sun kubuta salin alin.”
Dokta Ahmed ya ce hare-haren da ake kai wa makarantu a yanzu ya zama wani babban kalubale na kasa da ya bukatar kulawa ta gaggawa duba da tasirin da yake da shi a kan sha’anin ilimi a Arewacin Najeriya.
Yana cewa, “a yanzu mutane da dama ba za su so turo yaransu makaranta ba a yayin da wasu makarantu suke a rufe saboda fargabar za a iya kawo musu hari.”
“Wannan zai kawo babban gibi a tsakanin ’ya’yan talakawa da na masu hannu da shuni kuma zai kara haifar da wariya da rashin daidaito da kuma karin talauci.”
“A yanzu wannan lamari ya kara rage sha’awar neman ilimi a Arewacin Najeriya, kuma muddin aka samu wata tangarda a sha’anin ilimi, to kuwa matsala ce za ta kunno kai musamman talauci, ci baya da rashin tsaro saboda mutanen da ba su da ilimi sun fi saurin jefa kansu cikin harkoki na ta’ada,” in ji Dokta Ahmed.