✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin rushe Majalisar Zartaswar Jihar Bauchi — Bala Mohammed

Bana son aiki da wadanda basu fahimci mece ce siyasa ba.

Gwamna Bala Mohammad na Jihar Bauchi ya fayyace dalilinsa na sauke dukkanin ’yan Majalisar Zartaswa na Gwamnatinsa daga mukamansu.

A Larabar da ta gabata ce Gwamnan ya sallami dukkan Kwamishinoni tare da rushe Majalisar Zartaswar Jihar Bauhci da sauran masu rika da mukaman siyasa da suka hada Sakataren Gwamnati, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati da dukkan Mashawarta na Musamman.

Sai dai Gwamnan a jiya Asabar yayin gabatar da jawabansa na Ranar Dimokuradiyya a Karamar Hukumar Zaki da ke Jihar, ya ce ya raba gari da manyan jami’an gwamnatin ne saboda wargi da suka kawo masa cikin al’amuran da suka shafi siyasar jihar.

A cewarsa, wadanda ya sallama basu fahimci yadda siyasa take ba.

Ya ce ya rushe Majalisar Zartaswar Jihar da zummar kafa sabuwa domin bai wa wasu damar hidimta wa Jihar domin ciyar da ita gaba.

Ya ce, “wadanda na sallama, sun kasa lakantar yadda ake gudanar da siyasa, saboda haka ba zan iya ci gaba da aiki da irin wadannan mutanen ba.

“Shi ya sa kawai na yanke shawarar samun wasu ’yan siyasar na hakika wadanda suka lakanci harkokinta domin mu yi aiki tare wajen ciyar da Jihar Bauchi gaba,” a cewar Gwamnan.