✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da ’yan Najeriya ke fuskantar tsangwama a Dubai —Gwamnati

Wasu ’yan Najeriya sun tayar da tarzomar saboda tsaurara dokokin samun ta biza.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi karin haske kan yadda ake musgunawa ’yan Najeriya a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

A makonnin baya-bayan nan dai kafafen sada zumunta sun yi ta yada rahotannin cin zarafin da ake yi wa ’yan Najeriya a kasar.

Da take tsokaci kan batun, Shugabar Hukumar ’yan Najeriya mazauna Kasashen Waje (NIDCOM), Misis Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa, a kwanakin baya Hukumomin Kasar UAE sun fitar da sababbin ka’idoji na neman biza ga mutanen kasa da shekara 40.

Ta ce, da yawa daga cikin ’yan Najeriya a yanzu suna kokarin kauce wa ka’idojin ta hanyar neman takardar izinin zama tare da iyalansu “biza ta iyali,” maimakon ba da haske kan irin bizar da suke nema.

Ta bayyana cewa, dole ne a samar da bayanan banki na gaskiya na tsawon watanni shida, da bayanan masauki da tikitin dawowa, idan an iso kasar.

Aminiya ta rawaito cewa, hukumomin UAE sun tsaurara dokokin ba da takardar zama ta biza ga ‘yan Najeriya biyo bayan tarzomar da wasu ’yan Najeriya suka yi a kasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Dabiri-Erewa ta ce, “Ku tuna gargadin da aka yi a baya-bayan nan. A yanzu dai gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta bullo da wani sabon tsarin biza kuma ta daina bayar da bizar yawon bude ido ga wadanda suke kasa da shekaru 40, sai dai wadanda ke neman bizar iyali.